MASARI YA GANA DA BUHARI KAN MATSALAR TSARO YA TABBATAR MAI DA CEWA KOME ZAI KWARANYA DA GAGGAWA
Gwamnan jihar Katsina Rt. Hon Aminu Bello Masari ya gana da shugaban kasar Nijeriya Muhammadu Buhari a fadar sa da ke Abuja a daren jiya kan matsalar tsaro, musamman mummunan harin da 'yan bindiga suka kai a wani kauye na karamar hukumar Batsari.
Ofishin yada labarai na gidan gwamnati wato Katsina Media and Publicity ya rawaito cewa, zaman an yi shi ne na sirri wanda ya kwashe sama da awanni hudu ana ganawa. Bayan gama ganawar Masari ya tabbatar wa manema labarai da cewa an cimma nasarar abin da aka tattaunawa.
Gwamnan Ya fadawa manema labarai cewa, tsaro a jihar Katsina yana fuskantar barazana, kuma ya kara da cewa saboda matsalar tsaro da jihar ke fama da shi, za a fuskanci karancin noma a kananan hukumomin da suke fuskantar barazanar. Ya bayyana cewa wadannan 'yan bindigar kan su hade yake kuma kome suna yin sa ne a tsare, sun san inda suka nufa kuma sun san hanyoyin shamta wajen gudanar da munana aiyukansu.
Ya kuma tabbatar da cewa shugaban kasar ya fahimci irin matsalar da jihar take ciki, kuma ya bada tabbacin cewa shugaban kasar ya sha alawashin kawo hanyoyin magance matsalar da wuri.
@Katgovmedia ta rawaito cewa gwamnan ya yi kira ga al'umma da su yi hakuri su kwantar da hankalin su, ya kuma kara jajantawa al'ummar kan wannan rashi da suka yi da kuma abin da rashin ya haddasa, ya kuma tabbatar masu da cewa, nan ba da dadewa ba wadannan hare-hare za su kawo karshe a jihar baki daya.
Ibrahim M Abdullah
Director General
Media & Publicity
23rd May 2019
Saturday, May 25, 2019
MASARI YA SA HANNU KAN DOKAR KASHE BARAYIN SHANU, MASU GARKUWA DA MUTANE

Gwamnan jihar Katsina Rt. Hon Aminu Bello Masari ya sanya wa dokar da aka yi wa kwaskwarima wadda ta bada damar a kashe duk wani wanda aka kama ya saci shanu ko ya yi garkuwa da mutane hannu.
@Katgovmedia ta rawaito cewa gwamnan ya kuma rattaba hannu akan duk wanda kotu ta tabbatar da ya aikata laifin fyade a yi masa daurin rai da rai, sannan kuma ya biya diyya ga wadda ya aikatawa laifin.
Da ya ke jawabi a wajen taron sanya hannun kan sabbin dokokin gwamnan ya bayyana cewa akwai bukatar a samu sabbin dokoki da zasu dace da yanayin tabarbarewar tsaron da ake fama da shi a wannan jiha.
Ya bayyana cewa wanna dokar an kirkireta ne kawai a bangaren masu Garkuwa da mutane da barayin shanu da kuma masu aikata laifi fyade da sauran laifuka masu alaka da wadannan. Ya bayyana cewa ya yanke shawarar daukar wannan doka da muhimmanci da kuma aiwatar da ita ga duk!wanda aka samu da aikata laifukan.
Sannan ya kara da cewa dokar ba za ta yi aiki ba ga wadanda aka riga aka yankewa hukunci kan wadannan laifuka, sai dai masu niyyar aikatawa daga yanzu.
In za a iya tunawa dai jihar Katsina na daya daga cikin jihohin Arewacin Nijeriya dake fama da matsalar tabarbarewar tsaro wadanda suka hada da barayin shanu da masu garkuwa da mutane da 'yan bindiga da sauran makamantansu.
Gwamnan dai ya je Abuja a ranar laraba domin ganawa da shugaban kasa domin kawo dauki da dawo da tsaro a cikin jihar Katsina kamar yadda ta ke a baya.
Director General
Katsina Media & Publicity

24th May 2019
Subscribe to:
Posts (Atom)