Saturday, May 25, 2019

MASARI YA GANA DA BUHARI KAN MATSALAR TSARO YA TABBATAR MAI DA CEWA KOME ZAI KWARANYA DA GAGGAWA

MASARI YA GANA DA BUHARI KAN MATSALAR TSARO YA TABBATAR MAI DA CEWA KOME ZAI KWARANYA DA GAGGAWA

Gwamnan jihar Katsina Rt. Hon Aminu Bello Masari ya gana da shugaban kasar Nijeriya Muhammadu Buhari a fadar sa da ke Abuja a daren jiya kan matsalar tsaro, musamman mummunan harin da 'yan bindiga suka kai a wani kauye na karamar hukumar Batsari.

Ofishin yada labarai na gidan gwamnati wato Katsina Media and Publicity ya rawaito cewa, zaman an yi shi ne na sirri wanda ya kwashe sama da awanni hudu ana ganawa. Bayan gama ganawar Masari ya tabbatar wa manema labarai da cewa an cimma nasarar abin da aka tattaunawa.

Gwamnan Ya fadawa manema labarai cewa, tsaro a jihar Katsina yana fuskantar barazana, kuma ya kara da cewa saboda matsalar tsaro da jihar ke fama da shi, za a fuskanci  karancin noma a kananan hukumomin da suke fuskantar barazanar. Ya bayyana cewa wadannan 'yan bindigar kan su hade yake kuma kome suna yin sa ne a tsare, sun san inda suka nufa kuma sun san hanyoyin shamta wajen gudanar da munana aiyukansu.

Ya kuma tabbatar da cewa shugaban kasar ya fahimci irin matsalar da jihar take ciki, kuma ya bada tabbacin  cewa shugaban kasar ya sha alawashin kawo hanyoyin magance matsalar da wuri.

@Katgovmedia ta rawaito cewa gwamnan ya yi kira ga al'umma da su yi hakuri su kwantar da hankalin su, ya kuma kara jajantawa al'ummar kan wannan rashi da suka yi da kuma abin da rashin ya haddasa, ya kuma tabbatar masu da cewa, nan ba da dadewa ba wadannan hare-hare za su kawo karshe a jihar baki daya.

Ibrahim M Abdullah
Director General
Media & Publicity
23rd May 2019

No comments:

Post a Comment