Gwamnan jihar Katsina Rt. Hon Aminu Bello Masari ya sanya wa dokar da aka yi wa kwaskwarima wadda ta bada damar a kashe duk wani wanda aka kama ya saci shanu ko ya yi garkuwa da mutane hannu.
@Katgovmedia ta rawaito cewa gwamnan ya kuma rattaba hannu akan duk wanda kotu ta tabbatar da ya aikata laifin fyade a yi masa daurin rai da rai, sannan kuma ya biya diyya ga wadda ya aikatawa laifin.
Da ya ke jawabi a wajen taron sanya hannun kan sabbin dokokin gwamnan ya bayyana cewa akwai bukatar a samu sabbin dokoki da zasu dace da yanayin tabarbarewar tsaron da ake fama da shi a wannan jiha.
Ya bayyana cewa wanna dokar an kirkireta ne kawai a bangaren masu Garkuwa da mutane da barayin shanu da kuma masu aikata laifi fyade da sauran laifuka masu alaka da wadannan. Ya bayyana cewa ya yanke shawarar daukar wannan doka da muhimmanci da kuma aiwatar da ita ga duk!wanda aka samu da aikata laifukan.
Sannan ya kara da cewa dokar ba za ta yi aiki ba ga wadanda aka riga aka yankewa hukunci kan wadannan laifuka, sai dai masu niyyar aikatawa daga yanzu.
In za a iya tunawa dai jihar Katsina na daya daga cikin jihohin Arewacin Nijeriya dake fama da matsalar tabarbarewar tsaro wadanda suka hada da barayin shanu da masu garkuwa da mutane da 'yan bindiga da sauran makamantansu.
Gwamnan dai ya je Abuja a ranar laraba domin ganawa da shugaban kasa domin kawo dauki da dawo da tsaro a cikin jihar Katsina kamar yadda ta ke a baya.
Director General
Katsina Media & Publicity
Ibrahim M Abdullah
No comments:
Post a Comment